'Yan sanda sun cafke mutuminda yakewa Atiku Abubakar Barazanar kisa

Rundunar 'yan sandan Nigeria sun cafke wani mutum dan kimanin shekara 43, mai suna Augustus Akpan wanda aka zargi da yin barazanar kisa ga tshohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da iyalan gidansa idan har bai janye daga neman tsayawa takarar shugabancin kasa ba.

Mai magana da yawun 'yan sanda Jimoh Moshood yace" Mutumin dan asalin kauyen Edemaya a karamar hukumar Ikot Abasi dake jihar Akwa Ibom. 

Ana tumumar Akpan ne da aika sakon wayar salula dake dauke da kalaman barazanar kisa ga rayuwar Alh Atiku Abubakar, matarsa da kuma diyarsa. 

Cikin zarge zargen da ake tumumar Akpan dasu harda barazanar fyade ga daya daga cikin matan Atiku wato Jennifer da kuma 'ya'yansa fatima da Maryam idan har bai janye aniyar tsayawa takara a jam'iyyar PDP ba. 

'Yan sanda sun shaida gano wayar salula mai suna Samsung Galaxy S6 plus da kuma layin waya da akayi amfani dasu wajen aika sakon barazanar ga iyalan Atiku Abubakar.

Acikin sakon an rubuta cewa:

"Koda Buhari bazai ci zabe ba, mun sani kaine babba acikin 'yan takarar jam'iyyar PDP kuma muna tabbatar maka idan baka janye ba zamu harbo jirginka tun daga sararin samaniya kuma zamu watsa acid a fuskarka da iyalanka. 

"Ya kai Atiku Abubakar kasani kuma ka rubuta ka aje. idan har baka janye ba zakaga abinda zai faru dakai, kajira kawai kaga abinda zai faru, Mun san inda kake zama kuma munsan inda 'ya'yanka suke zuwa yawo.

Akpan ya amsa laifinsa kuma yace yayi haka ne saboda abaya yayita kokarin samun hanyarda karbi kudi daga hannun Atiku amma abin yagagara shiyasa yayi masa barazana.

Rundunar 'yan sanda ta kama Augustus Akpan ne a bisa hanyar ake zuwa ibadan daga jihar Lagos.