Majalissar ta dau matakin gyara dokokin ne bayan kin amincewa da fadar shugaban kasa tayi da wasu dokokin da suka aika mata da ta sa hannu akansu.
Shugaba Buhari yaki amincewa ne sakamakon wasu kura kurai da yake ganin sunyi wajen shirya dokokin zaben wanda akayiwa gyare gyare a shekarar 2010.
Shugaban kwamitin tsara dokokin zaben Senata Sulaiman Nazifi yace sun karbi korafin shugabab kasar ne saboda karbar gyara da kuma nunawa alummar Nigeria cewa wannan aiki da suke domin 'yan nigeria ne kuma bazasu bawa jamarsu kunya ba.
Senata Nazifi yace wannan shine karo na 4 da suke gyara dokokin wadanda shugaba Buhari sau 2 yana mayar musu takardun da nufin sun tafka kura kurai aciki. Amma nayi imani cewa duk wannan abu da muke munayi ne da nufin wakiltar 'yan kasa da alhakinsu ya rataya wuyanmu.
Shugaba Buhari ya aika sako ga shugabannin majalissun 2 Senata Bakola Saraki da Speaker Yakubu Dogara yana mai sanar dasu dalilai da suka sanya yaki amincewa da dokokin.

