yadda zaka samu bonus din 1.5GB kyau a layin Airtel


A ‘yan kwanakin nan da suka gabata, ana ganin cewa Glo shine layin da yafi ko wane layi a Nigeria saukin data, a inda da N1000 zaka iya sayen 3.2GB a wata daya. Yau kuma mun zo muku da wani babban albishir na wani tsari mai suna DATA DEAL da Airtel suka zo da zaka iya samun 1.5GB data kyauta a matsayin bonus idan ka sayi 750MB a kan N500 kacal! Ka ga ke nan ka sayi ta N500 sun baka bonus ta N1000! Ka ga ke nan ka tashi da 2.25GB a N500!

Shi dai wannan tsari yana yin sati biyu ne kafin datar ta yi expire. To mi kuma kake jira?

Sai ka dauko sim dinka na Airtel ka kakkabe masa kura, ka sanya shi a wayarka, ka bi wadannan matakan domin moriya da wannan garabasa:
1. Ka loda katin da ya kai darjar N500 a cikin layin naka
2. Ka sanya wannan code din *418*2#
Da zaran ka sanya wannan code shi ke nan zasu turo maka da sakon cewa ka samu nasarar shiga wannan tsari.

Idan kana karuwa da wadannan kasidoji da muke kawo muku, to kayi sharing din shafinmu a Facebook, Whatsapp da sauransu, domin wasu suma su amfana.
Idan kana bukatar tofa albarkacin bakinka game da wannan kasidar, ko kuma kana da wata tambaya to karka yi wata-wata kayi comment a nan kasa. Ga duk mai bukatar samun kasidunmu ta hanyar Whatsapp shima ya iya yin comment da lambarshi.