sannan wajen canjawar a guji sanya 123456 ko sunan ka, ko kuma lambar wayarka, sunan budurwar ka, ko unguwar ka, a’a yana da kyau ka sanya harufa da kuma lambobi, kai harma da symbols kamar @”-+, sannan kada ka yarda ka sanar da wani wannan password din naka,
Sannan a kula kada kayi amfani da password guda daya a dukkan abubuwanka misali a Email dinka da kuma facebook din ka da sauran abinda kake budewa duk su zama iri daya domin hakan zai baiwa wasu damar yin awon gaba da account dinka,
2. sanya Karin email akan account dinka a kalla ina bada shawarar kayi adding email kamar guda uku (3) akan account dinka kaga kana da cikakken iko akan account dinka duk wani motsi ko wani yunkuri da akayi kai tsaye zaka gani,
Sannan a setting na email din ka mayar dashi babu wanda zai iya ganin su sai kai kadai “only me” a yaren facebook,
3. Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki kana samun sakonni acikin ta da yawan mu lambobin da muka bude facebook dasu mun rasa layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar daga kan fb din mu canza ta da lambar da muke da ita a yanzu, rashin yin hakan zai bamu matsala don haka idan kasan ka rasa layin ka to ka canza lambar layin ka na yanzu domin ka cigaba da samun sakonnin facebook,
4. Ka sanya “Login Approval” a account din ka yadda zaka sanya shine ka bi wannan hanyar kaje :Home -> Account Settings -> Security -> Login Notification sai ka mai da shi “Enable”
Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na account din ka sannan idan zakayi login dole sai an turo maka da code ko kuma kayi approving ta wayarka idan android ce, sannan anan bangaren zaka iya samar da “code generator” ta yadda zaka samar da wani code wanda kai ka dai ne ka sanshi idan kazo yin login bayan password to shi ma zaka saka shi,
5. Sannan zaka iya zabar wasu amintattu daga friend dinka kamar Grantor kenan ka sanya su, suma zasu iya baiwa account din ka kariya,
6. Ka samar da tsayayyiyar browser da kake hawa facebook, kada ka zama yau ka ari wayar wancan ka hau gobe ka ari ta wancan, sannan a daina yin saving din password a browser saboda zaka iya yadda wayar ka, ko kuma a dauke maka ita, mu samman a wannan lokacin da ake yawan kwace kaga wani zai iya hawa, sannan facebook zasu iya yi maka blocking saboda yawan yin hakan,
7. Ka dinga yin log out duk sanda ka hau idan zaka sauka,
8. Kada ka baiwa wani ko wata bayanan ka na yin login a account din ka ko wani web site,
9. Kayi tunani kafin ka danna link, zaka ga ance ka danna link, to ka fara yin tunani kafin ka shiga, misali ace ka danna kaga abinda zai faru ko makamantan hakan, ko idan ka shiga sai kaga ance ka saka password dinka to duk irin wannan sai a kiyaye,
10. Kayi login a www.facebook.com ka wai
www.fb.com kada kayi login a facebook ta kan wani site daban ba wannan ba, ko application wanda ba ingantacce ba,
11. Ka dinga yin updating din browser din ka ko application din ka,
12. ka dina installing anti virus a wayar ka ko a computer da kake amfani da ita,
13. ka daina yawan tura Requesting ko yawan yin accepting ka kula wajen karbar wanda baka san shi ba, yana da kyau ka duba propile din sa kafin kayi accepting din sa,
14. Ka daina yawan yin sharing na wani link da baka tantance shi ba,
15. ka daina hade facebook account dinka da ko wane shafukan internet, zaka ga da yawa daga website ana yin register din su ta facebook mai makon kayi da email sai kayi da facebook shima wannan ya kamata ayi tunani sosai kafin aiwatarwa,
16. Kada ka yi wani psoting wanda ya sabawa wadansu to idan suka yi ta yin reporting din sag a facebook su ma zasu yi blockin din account din ka, YADDA ZAKA KARE FACEBOOK ACCOUNT DIN KA DAGA BLOCKIN KO HACKING

