Yadda aka gudanarda wasan zakarun turai 2018

Daniel Sturridge, wanda shi ne ya maye gurbin Firmino a kungiyar ta LIverpool ne ya ci kwallo ta farko, inda shi kuma James Milner ya zura kwallo a ragar PSG bayan da aka ba Liverpool bugun fenariti.

Amma Thomas Meunier ya farke wa Paris St Germain kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma da alama wasan na hannun Liverpool ne bayan da Neymar da Mbappe suka kasa tabuka komai.

Alkalin wasa ya kuma hana wata kwallo da Mohammed Salah ya ci, saboda ya yi wani laifi a lokacin.

Wannan wasan na yau ya nuna cewa Liverpool a shirye ta ke ta fuskanci dukkan kalubalen da ke tafe a kakr wasa ta bana.

PSG kuwa ba su tabuka wani abun a zo a gani ba, duk da cewa suna da kwararru kuma shahararrun 'yan wasa kamar Neymar da Angel di Maria da Edison Cavani da kuma Mbappe, wanda shi akalla ya kwaci kansa bayan da ya zura wa Liverpool kwallo a lokacin da wasan ya koma 2 - 2.
Georginio Wijnaldum na LIverpool ne aka zaba a matsayin dan wasa da yafi kokari a wasan na yau.

Liverpool's next Champions League game is away to Napoli - who drew 0-0 away to Red Star Belgrade in their opening Group C game - on 3 October (20:00 BST).
Liverpool za ta tafi Italiya ne domin buga wasanta na gaba da kungiyar Napoli ranar 3 ga watan Oktoba, inda Napolin ta yi canjaras da Red Star Belgrade a wasanta na farko a yau.

Source: BBC HAUSA