WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH (S.A.W)

Manzon Allah (s.a.w) yace:
"Waye zai karbi wadannan kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi amfani da su, ko ya sanar
da wanda zai yi amfani da su"
Sai Abu Huraira (R.A) yace Ni zan karba ya Ma'aikin
Allah (S.A.W)

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya rike hannu na yace min:-
1. Ka guji aikata sabo, zaka zamo wanda yafi kowa bauta a cikin mutane.
2. Ka yarda da abinda Allah Ya baka, zaka fi kowa
arziki cikin mutane.
3. Ka kyautata wa makobcin ka, zaka zamo (cikakken) Mumini.
4. Ka so wa mutane abinda kake so wa kanka, zaka kasance (cikakken) Musulmi.
5. Kada ka yawaita dariya, domin yawan Dariya na
kashe zuciya.

MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA RIKE SU KO KA SANAR DA WANDA ZAI YI AMFANI
DA SU.
IDAN KA TURA WA YAN UWA MUSULMAI BAKA SAN WA ZAI YI
AMFANI DA SU BA, KAGA KA SAMU LADAN
MUTANE MASU TARIN
YAWA.

Allah bamu iKon kiyayewa.