Wani mutum yayi tattaki a kafa tun daga Lagos zuwa Abuja don nuna rashin jindadin mulkin Buhari

Bayan kwashe kwanaki 34 da wani mutum yayi yana tafiya a kafa tun daga Lagos da nufin nuna rashin dacewar komawar shugaba Buhari karagar mulki a 2019, Yanzu haka mutumin ya iso birnin tarayya Abuja.

A wata hira da akayi da mutumin mai suna Munlaila ya bayyana cewa dalilinsa nayin wannan tafiya shine don nuna rashin tsari ga irin salon mulki da Muhammadu Buhari ke tafiyarwa.

Yace " Acikin tafiyata na shiga garuruwa dayawa naga yadda mutane ke cikin yunwa da wahala sakamakon rashin cika alkawarinda wannan gomnati ta dauka. Mutane dayawa sun goyi bayana wannan tafiya tawa yayinda wasu ke tambayata ko inayiwa wata jam'iyya aiki ne. Ni kuma na basu amsa da cewa babu wata jam'iyya da nakewa aiki, inayi ne don matasan Nigeria wadanda nake ganin sunfi cancanta da mulkin Nigeria.

Munlaila wanda ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar PDP, Ya kara da cewa "A irin halinda naga mutanen Nigeria ke ciki gaskia babu wanda yadace da mulkin Nigeria kamar ATIKU ABUBAKAR. Idan Atiku ne ke rike da kasarnan na tabbata 'yan Nigeria zasu samu jindadi da walwala.

Mutane na cigaba da sharhi a kafafen sadarwa musamman Facebook. Saidai haryanzu bangaren gomnatin Nigeria basu ce uffan ba kan zarge zarge da wannan matafiyi yayi ba.