Munyi nazari domin zakulo muku wasu yan takarar shugaban kasa da suka sayi fom din takara guda biyu watakila don gudun kar suyi biyu bubu a zaben dake tafe.
1. Senata Rabiu Kwankwaso ya sayi fom din takarar shugaban kasa da kuma senata.
2. Senata Bakola Saraki zai yi takarar shugaban kasa da kuma senata.
3. Senata Ahmed Makarfi zaiyi takarar shugaban kasa da kuma senata.
4. Ibrahim Hassan Dankwambo ya sayi fom din shugaban kasa da kuma senata.
5. Aminu Waziri Tambuwal ya sayi fom din shugaban kasa da kuma Gomna.
6. Kabiru Turaki zaiyi ya sayi fom din takarar shugaban kasa da senata.
7. Sule Lamido ya sayi fom din shugaban kasa da senata.
Wata majiya tace Alh. Atiku Abubakar kadai wanda ya sayi fom guda 1 masu neman takarar shugaban kasa a jamiyyar PDP mai adawa a Nigeria.
Jamiyyar PDP itace tafi kowace jamiyya yan takara musamman na shugaban kasa saidai kuma tana fuskantar kalubale yayinda zata gudanarda zaben fidda gwani.
Siyasar Nigeria tana kara tsamari yayinda Zaben 2019 yake kara matsowa.