Shugaba Muhammadu Buhari ya samu kyakyawa tarba daga babban shehin darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Shugaba Buhari yakai ziyarar ne don taya malamin murnar cikar shekararsa 94 a duniya.
Dayawan zuriar malamin 'Ya'ya da jikoki tareda dalibai ne sukai gangamin tarbar shugaban a gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi dake Kaduna.
Saidai ziyarar tasamu cece-kuce a kafafen sada zumunta yayinda wasu ke ganin ziyarar shugaban matsayin wata dabarar siyasa domin samun goyon bayan malamin.



