Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi fom din tsayawa takara karkashin jamiyyar APC.
Shugaba Buhari ya tarbi wasu jajirtatun matasa wadanda sune sukai hadakar kudi makudai kimanin naira milyan 45 suka saya masa fom din a hannun jam'iyya.
An karbi fom din ne ayau talata da misalin karfe 11:30am a fadar shugaban kasa Villa dake Abuja.
Wani hazikin matashi mai suna Sunusi Musa wanda shine shugaban kungiyarda ta sayi fom din wato (Nigeria consolidation ambassadors network NCAN) shine ya mikawa Muhammadu Buhari fom din yayinda wasu 'yan uwa matasa na kungiyar suka masa rakiya zuwa fadar shugaban kasa. Daya daga cikin wadanda suka rakashi akwai wani matashin malamin jami'ar jihar Yobe wato Dr. Sheriff Almuhajir wanda sananne ne a shufukan sada zumunta musamman kafar sadarwar Facebook.
Karbar fom din ta samu rakiyar wasu manyan yan siyasa da kuma jiga jigan jam'iyyar APC wadanda sukai marhabin da abinda suka kira aikin alkhairi da matasan sukayi don nuna goyon baya ga irin rawarda gomnatin shugaba Buhari ke takawa a fanni dadama na cigaban Nigeria.
Tun bayan sayan fom din aketa cecekuce a kafafen sadarwa inda wasu masu sharhi kan lamuran siyasa ke ganin sayawa dan takara fom kamar wani nau'i ne na ci baya a tsarin mulkin demokradiyya.


