A cikin wannan makon da muke ciki ne wata jarida ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta rufe account din dan takarar gomnan jihar Osun, Senata Ademola Adeleke tareda account din wasu iyalansa ciki harda Shahararen mawakin Nigeria David Adeleke wanda akafi sani da Davido.
Bayan rade radin ya cika gari ne sai kuma aka jiyo mai magana da yawun hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya shaidawa manema labarai cewa zancen ba gaskia bane farfaganda ce ta 'yan siyasa domin batanci ga hukumar.
Wilson yace a irin wannan lokaci da siyasa ke kan guguwarta labaran karya suna yawaita. Wasu 'yan siyasar kuma suna amfani da labaran don cimma wasu bukatunsu na siyasa.
Yakara da cewa sukansu wadanda sukayi zargin 'yan jamiyyar PDP ne kuma basu da wata shaida akan lamarin. Sannan yakamata mutane suyi hattara don gujewa karbar labaran karya.
Wannan shine Karon farko da irin wannan badakalar zargi da faru da mawaki Davido kuma haryanzu baiyi magana ba watakila don kauracewa sanya kwakwanto a zukatan masoyansa.


