Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta kara yawan kwanakinda ta fitar domin sayan fom din takara da kuma mayar mata bayan an cike fom din.
APC ta fara sayarda fom din ne tun cikin watan August daya gabata sannan ta bayyana rufewa a ranar 11 ga watan Septemberda muke ciki.
A wata sanarwa da sakataren jamiyyar ya fitar yace an sauya ranar rufewa daga 10 zuwa 11 ga watan ne saboda sauran yan takara da basu gama cike fom din ba su samu damar mayarwa kafin a rufe.
Za'a rufe sayarwa da mayarwa ne a ranar 11 ga watan September.
Za'a rufe saya da karbar fom din takarar jam'iyyar tun daga kan shugaban kasa, Gomna, Majisun tarayya, Majalisar jiha.
Mutane dayawa ne suka sayi fom din takarar jam'iyyar akowane mataki idan aka cire shuganan kasa da babu wanda ya nuna sha'awar tsayawa bayan Muhammadu Buhari.

