Tsohon gomnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya fice daga jamiyyar PDP a bayan rushe shugabanninta na jiha da kuma dora shugabannin rikon kwarya da jam'iyyar tayi acikin wannan mako.
A kwanakin baya Mallam Shekarau yayi wata magana bayan komawar Senata Rabiu Kwankwaso cikin PDP. Shekarau yace zasuyi aiki tareda Kwankwaso kuma babu wata sabuwar gabar siyasa tsakaninsu sai gashi kuma tun ba'ayi nisa ba sun raba gari harta kaiga shekarau ya fice yabarwa Kwankwaso jam'iyyar.
Kafin faruwar haka dama masu sharhi kan al'amuran siyasa sun ayya hadewar jigajigan biyu Shekarau da Kwankwaso matsayin wata hadakar bukata wacce ba lalle ta tabbata ba sabida yadda suka jima suna adawa da juna a siyasance saigashi kuma ta faru.

