Senata Joshua Dariye ya sayi fom din ne dukda yana tsare a gidan yarin kuje bayan an yanke masa hukuncin daurin shekara 14 sakamakon aikata laifuka daban daban wadanda suka hada da baba kere da dukiyar alumma.
Bayanin sayan fom din ya fito ne daga hannun mai baiwa senatan shawara Itauna Dinka.
An yankewa senatan hukunci ne a ranar 12 ga watan June, a babbar kotun Fedaral High Court dake birnin tarayya Abuja.
Hukumar EFCC ce ta kama senatan bayan wani bincike data gano a 2007 wanda aka zargeshi da sauta akalar wasu makudan kudaden gomnati kimanin N1.126 billion zuwa Account din wani kamfaninsa mai suna evenezer reither Ventures.

