An samu babbar hatsaniya awajen gudanarda zaben fidda gwanin dan takarar gomna a jam'iyyar PDP.
Zaben ya gudana ne a gidan gomnati dake fadar jihar Gombe.
Hatsaniyar ta faru ne bayan fara kada kuri'a da akayi wanda deligate din Akko Local Govt suka fara bayan gomna Ibrahim Hassan Dankwambo ya jefa tashi kuri'ar ya fice daga dakin taron.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya samu asali ne inda wasu deligate ke ganin ba'a basu dama suna kadawa zabinsu kuri'arsu.
Deligate din ne suka fara rikicin kafin daga bisani wasu manya kamar Senata Bayero Nafada da Ahmad Walama suka hautseni hartakai ga Bayero ya wankawa Walama Mari hakan yasa wajen yakara daukar hatsaniya datayi sanadin fasa akwatunan zaben.
Bayan hayaniyar an kora kowa gida ba'a kammala zaben ba.

