Sabuwar jarumar kannywood Surayya Aminu

Surayya Aminu itace jaruma da ta shigo masana'antar fina finan Hausa acikin wannan Sabuwar shekara da muke ciki. 

Surayya haifafiya ce jihar Kaduna kuma a kaduna ta tashi tayi makaranta harya zuwa yanzu a jihar Kaduna take zaune. 

Jarumar ta shigo masana'antar da kafar dama yayinda darktoci da kuma furodusoshi sukaita marhabin da shigowarta a kafafen sadarwa musamman Instagram.

Ga dukkan alamu jarumar ta fito ne ta hannun wasu masu shiya fina finai na jihar kaduna saidai kuma alamu sun nuna tafison alaka da jarumin jarumai Ali Nuhu watakika ko don ganin yadda masu kallo ke karbar jarumai da suka fito daga hannun jarumin Ali Nuhu nan da nan sai tauraruwar jarumi ko jaruma ta haska matukar alakarta da FKD ta kusa ce. 

Kwanannan ake sa ran za'a fara daukar sabbin fina finai tareda sabuwar jarumar.