Pogba bazai cigaba da zama kaftin ba a Man United -Mourinho


Rikici yana kara ruruwa tsakanin dan wasa Paul Pogba da maigidansa Jose Mourinho..

Jose Mourinho wanda shine Kocin klub din Man United yace Pogba bazai cigaba da zama Matsayin Kaptin a kungiyar ba.

Mourinho yace "Pogba ya bugawa kungiyar wasa matsayin skifa lokacinda kaftin din klub din Antonio Valencia bayanan. Pogba ya buga wasa 3 a wannan sizin wasannin sun hada da: Leicester City da kuma wasan Brighton a premier league sannan sai wasan Champion league na kananan zakarun turai.

Rahotanni sun ce Mourinho ya bayyanawa dan wasan Pogba mai shekaru 25 cewa baya aikin kaftin yadda yakamata kuma Man United tana sama da kowa.

Man U bata sanya sunan Pogba cikin wadanda zasu buga mata wasan Tuesday's league da zaayi ba saidai an umarci dan wasan yacigaba da zama cikin jerin wadanda aka baiwa hutu maimakon yazauna kamar ankoreshi.

Yanzu haka dai dan wasa Paul Pogba ya fara shirin tsallakewa zuwa Barcelona tun kafin a kammala masa takardar tranafer.

Pogba ya koma Manchester United ne bayan nasarar daya samu a wasan duniya da ya bugawa kasar faransa lokacin ne Man United ta sayoshi akan farashin kudi dalar amurka $116 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Juventus.