Akanta jenaral na Nigeria Ahmed Idriss ya bayyana cewa gomnati zata biya ma'aika albashinsu dukda irin jajin aikinda suka shiga.
Ahmed Idriss yace " Munyi iya kokarinmu wajen aiki tareda shugaban kasa don biyan kowane ma'aikaci albashinsa akan lokaci kamar yadda muke biya a baya kowane 25 ga wata saidai hakan yacitura sakamakom wasu matsaloli da muke fuskanta wanda a wannan watan ma hakan bazata yiwu ba.
Ahmed yace " Bazai yiwu mu sake Albashin wannan watam cikin sauki ba saboda duk manyan ofisoshi da za'a gudanarda biyan albashin a rufe suke sakamon yajin aiki.
"Bamu kadai bane keda alhakin sake albashi ba dole sai mun tura zuwa ministrin kudi na Nigeria da kuma sauran wasu ma'aikatu da sukeda aikinsu kafin mu aiwatar.
"Ko safiyar yau munyi kokarin zuwa ofis amma daga isarmu mu samu kofofin wuraren aiki a garkame kuma babu yadda zamuyi muyi aiki ba'a ofis ba.
Ahmed Idriss ya kuma kara da cewa yakamata kungiyar kwadago tayi dubi da irin kokarin gomnatin shugaba Buhari wajen biyan hakki da kuma samarda walwala da jindadin ma'aikata a duk fadin kasar.

