Maman Taraba ta aje mukaminta na minista sannan ta fice daga APC

Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta ajiye mukaminta na minista ne sakamakon rashin jituwa da aka samu tsakaninta da babbar jam'iyyar APC mai mulki.

Rikicin ya faro ne tun lokacinda Aisha Jummai ta nuna goyon bayanta ga uban gidanta Alh. Atiku Abubakar wanda yake neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta PDP.

Ko a kwanakin baya lokacinda ake tantance 'yan takarar gomna, jam'iyyar APC ta umarci jami'anta da kada su tantance Aisha Jummai a jihar Taraba. Abinda baiyi mata dadi ba kuma ta nunawa jamiyyar rashin adalci ne haka gareta.

Hajiya Aisha Jummai Alhassan tshohuwar Senata ce wacce ta fito takarar gomnan jihar Taraba a shekarar 2015 karkashin jamiyyar APC saidai batayi nasarar lashe zaben ba, hakan yasa aka bata mukamin ministar mata bayan rantsarda shugaba Buhari akan karagar mulki.