Kungiyar kwado ta kasa ta janye yajin aiki da ta shiga tun ranar 27 wanda ya tsayarda abubuwa da yawa a duk fadin Nigeria.
Shugaban kungiyar yace sun dauki matakin jabye yajin ne saboda alkawari da gomnati tayi musu ba amsa bukatunsu cikin gaggawa.
Kungiyar tace idan har gomnatin kasar bata cika alkawarin ba dole zasu sake shiga yaji don kwatowa kananan ma'aikata hakkinsu na karin albashi.
Kwana biyu da shiga yajin aiki ne akanta genaral ya zayyana cewa bazasu iya biyan albashin wannan watan ba idan har ana yajin aiki saboda wuraren ayyuka a rufe suke.

