Ko yanzu na mutu naci ribar rayuwar aure -Fati Ladan

Fati Ladan tareda 'Danta. 
Fati ladan tsohuwar jarumar fina finan Hausa ce wacce ta jima ana damawa daita musamman a fina finan soyayya saidai daga bisani tayi aure a karshen shekarar 2013.

Fatima ta auri wani hamshakin dan kasuwa a Kaduna mai suna SHETTIMA wanda suka haifi d'a namiji guda 1 tare dashi.

Kafin shigarta harkokin fina finai tayi aure sau biyu wadanda Allah bai nufeta da zama a tareda mazajen ba. 

Fati ladan ta taka rawa mai yawa a fina finan Hausa har saida ta shiga sahun jarumai mata mafi shahara da kuma kyau a masana'antar Kannywood.

Jaruman fina finan Hausa dayawa sunyita dora hoton jarumar da 'Danta a kafafen sadarwa suna aika mata da sakon fatan alkhairi.

Tun bayan auren Fati Ladan ba'a sake jin duriyarta acikin wani lamari daya shafi harkar fina finai ba watakila tayi hakan ne don gudun matsala acikin zaman aurenta.