Shahararriyar jarumar fina finan Hausa MARYAM GIDADO ta samu karramawar girma daga masarautar Yakanaje dake wani garin Uke a jihar Plateau.
An baiwa Maryam Gidado babbar sarauta ne matsayin "Zinariyar Uke" wacce sarauta ce da ba'a baiwa wadanda ba yardaddun masarauta ba.
Jarumar ta samu karramawar ne bisa kwazo da kuma girmama masarautar da aka shaideta dashi.
Maryam haifafiya ce a Jos kuma haryau acikin Jos take rayuwa tareda yan uwa da 'ya'yanta wadanda ta baro a gidajen auren da tayi a shekarun baya.
Jarumar ta nuna farinciki da murnar wannan girmamawa da aka mata kuma tayita dira hotunan wurin bikin sarautar tana rubuce rubucen godiya ga masautar.
Jarumai dayawa maza da mata sunyita daura hotunan sarautar suma domin taya abokiyar sana'arsu murnar wannan karramawa.





