Zaben jihar Osunya dauki hankali sosai saboda yadda manyan yan siyasa sukaita cincirindo zuwa jihar don taya 'yan takararsu neman kuri'a.
yanzu haka jamaa sun fito kwansu da kwar kwata don jifa kuri'arsu saidai rahotanni suna cewa an samu amfani da kudi wajen sayan kuriu a wasu rumfunan zabe.
Yanzu haka daya daga cikin yan takarar gomnan jihar wato Senata Adeleke ya samu jefa kuriarsa.
Zabe yana tafiya daidai a jihar a yanzu haka bu wani rahoto na tashin hankali ko kuma rashin jituwa.
Ana ganin wannan zabe shine zai zama alamar yadda zaben 2019 zai kasance.
Zamu kawo muku rahotanni akan sakamakon zaben idan ya kammala a yau.

