Fitacciyar Jarumar fina finan Hausa Maryam Boot ta taya kaninta Amude Boot murnar karin shekara (Birthday) da ya yayi a watan August daya gabata.
Jarumar ta dora hotonsa a kafar sadarwa Instagram sannan ta rubuta sako ajikin hoton kamar haka:
"Dan uwana shine abokin kuruciyata nafi sabawa dashi fiyeda kowa, muyi wasa tare, muyi tsokana tare sannan muyi fada mu shirya don haka nakesonshi fiyeda komai a rayuwata.
Amude Boot shine yaron da daya fara fitowa a fina finai tun ana goyonsa kasancewar mahaifiyarsa Zainab Boot jaruma ce sannan dayawan yayyensa ma kamar Ramadan Boot da ita Maryam Boot duk jarumai ne wannan yasa ake ganin gidansu ya kyankyashe jarumai da baza'a manta dasu ba.
Hoton kuruciyar Maryam da Amude
Maryam da Amude a mota








