Ga abubuwa kadan da dabi'ar madigo ke haifarwa:
1. Sabawa addini ko kuma gamuwa da fushin ubangiji: Allah S.W.A ya tsarawa bayinsa yadda zasu sadu da junansu sannan ya haramtawa maza neman maza ko mace ta nemi mace don yanada kyau duk sabonda mutum zaiyi yaji tsoron Allah ya tuna cewa akwai azaba don gudun afkawa cikin rudin shedan.
2. Kamuwa cutar sida HIV ko kananan cutuka STDs: sakamakom wasu matan suna saduwa da maza kuma su sadu da mata ko su tsotsi wani bangare na dubura ko farji wanda hakan ka iya zama silar kamuwa da cutuka da dama.
3. Cutar Kibar jiki: Mata masu madigo sunada yiwuwar kamuwa da cutar kibar da kashi 52.8% fiyeda masu saduwa da maza wadanda keda yiwuwar kamuwa da cutar da kashi 45.3%.
4. Matsalar haihuwa:
Mata masu madigo suna da yiwuwar haihuwa ne kashi 30% kasa da wadanda ke saduwa da maza keda kashi 70% wanda hakan ya nuna cewa mace mai madigo ba lalle bane ta haihu koda tayi aure akwai yiwuwar bazataji dadin aure da namiji ba.
5. Damuwa, Rashin nutsuwa da yawan tunani:
Mace mai madigo tana fuskantar kalubalen zama cikin jama'a ko yawan tunani sakamakon rufe asirin abokan madigonta. Sannan akwai barazana mai yawa idan taje asibiti lafiyarta likata kan iya gane cewa 'yar madigo ce.
Dukda cewa haryaznu likitoci basu fadi takamaiman cutarda dabi'ar madigo take sanyawa ba amma zamu iya gane hatsarinsa bisa alkaluma da suka fitar na yiwuwar kamuwa da cutaka dayawa ciki harda CANCER da Kuma HIV.

