Buhari Mohammad Dankwambo ya fice daga jamiyar PDP mai mulkin jihar Gombe.
Buhari kanine ga gomnan jihar Gombe Alh. Ibrahim Hassan Dankwambo. Matashin yace ya bar PDP ne saboda sabani da suka samu da wansa Tolban Gombe akan rashin cika wasu alkawura da yayiwa jihar kuma bai cika ba.
Jihar ta dauki wani sauyi na siyasa inda ko akwanaki wasu jigajigai a APC sun kaura sun koma PDP bayan wata takaddama da suka samu a jamiyyar.
Wannan lamari yana zuwa ne yayinda gomnan jihar ke neman takarar shugabancin nigeria a karkashin jamiyyar PDP.

