Dalilinda yasa na zabi komawa jam'iyyar UDP -Senata Aisha

'Yar takarar gomna wacce ta akiye mukaminta na minista Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta bayyana dalilinda yasa ta fice daga jamiyyar APC.

Hajiya Aisha aika da wasikar barin aiki ga fadar shugaban kasa bayan ta fice daga jam'iyyar APC sakamakon kin tantanceta cikin jerin wadanda zasuyi takarar gomna a zaben fidda gwani da za'a gudanar.

Acikin wasikar data rubuta, Haj. Aisha ta bayyana rashin jindadinta ga matakinda mahukuntan jam'iyyar APC suka dauka akanta, kamar yadda tace "Dalilina na ajiye aiki shine, ina ganin bai kamata in cigaba da zama minista a karkashin mulkin APC tunda har biyayya da matsayina a jam'iyyar bai kai a tantanceni cikin 'yan takarar gomna ba.

"Na zabi komawa jam'iyyar UDP saboda soyayya karamar jam'iyya ce mai manufofi masu kyau. Sannan ina ganin hakan shine daidai a demokradiyya, yanzu fa talakawa sun waye babu ruwansu da wace jam'iyya kake halin mutum jarinsa.

Idan baku manta ba a kwanakin baya ne Hajia Aisha Jummai ta nuna goyon bayanta ga tshohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda shine ubangidanta a siyasa. Yana cikin dalilai da suka hassala shugabannin APC hartakai ga kin tantanceta.

Aisha Jummai Alhassan tshohuwar Senata ce wacce tayi tajarat

Ajiye aikin Maman Taraba ya jawo cece kuce musamman a kafafen sadarwa inda wasu ke ganin tayi daidai wasu magoya bayan APC kuma ke cewa "ALLAH RAKA TAKI GONA".