Buhari zai karbi fom dinda matasa suka saya masa naira milyan 45


Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi fom din tsayawarsa takara gobe talata da misalin karfe 11:30 na safe.

Taron zai gudana ne a sabon dakin taro BANGUET HALL dake villa fadar shugaban kasa dake Abuja.

Matasan nan a karkashin kungiyar NIGERIAN CONSOLIDATION AMBASSADORS NETWORK sune zasu gabatarwa shugaban kasa fom din da suka saya masa a adadin kudi naira milyan 45.

Sayan fom din ya samu caccaka daga dayawan matasa masu sharhi kan alumaran siyasa musamman a kafafen sadarwa na facebook da twitter. An ayyana karabar fom din takarar matsayin kamar wani nau i na cin hanci da siyasance.

Dukda sukar da sukar da aketa yiwa lamarin fadar shugaban kasa ta yanke shawarar karbar fom din daga hannun matasan.

Karbar Fom din zau samu rakiya daga wasu Gomnoni da senatocin jamiyyar APC domin nuna jindadin abinda matasan sukayi don nuna soyayya da goyon bayansu ga gomnatin shugaba Buhari da jamiyyar APC mai rike da madafun iko a nigeria.