Shahararen mawaki kuma jarumin fina finan Hausa Adam A Zango ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin zabinsa a zaben shekarar 2019.
Jarumin ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram a kusa da wani faifan videon sabuwar wakar shugaba Buhari da hadakar mawakan Hausa suka wallafa waka mai suna "Sakamakon chanji".
Adam A Zango yana daga cikin mawaka masu ra'ayin shugaba Buhari tun shekarar 2015 suke cikin tafiyar Buhari kuma yana amfanuwa da tafiyar saboda yadda suke alaka kut-da-kut da shugaban mawakan Buhari DAUDA KAHUTU RARARA.
Abaya 2015 Adam A Zango shine ya jagoranci bautukan wata wakar Buhari mai suna "Lema ta yage" hakazalika jarumin yasha fitowa a yana kiran masoyansa da su zabi Buhari bayan halartar wuraren taron Buhari ko jam'iyyar APC da yakeyi.

