Shahraren Jarumin fina finan Kannywood Adam A Zango ya aika wani sako da yake dauke da kalamanan neman gafara ga tshohon maigidansa Ali Nuhu.
Zango ya wallafa sakon ne tareda wani hoto a shafinsa dake kafar sadarwa ta INSTAGRAM.
Adam Zango ya rubuta sakon ne da bai wuce gajeruwar jimlar magana guda 2 ba.
Yace "Tuba nake sarki, gwiwowina a kasa"
Ga sakon kamar haka:
Tun bayan kafuwar Adam A Zango dai aka fara samun takun saka tsakaninsa da Ali Nuhu wanda mafi yawan sabanin yana farowa ne daga kan mabiyansu daga baya kuma sai suma su dauka.
An kwashe shekaru ana wannan takun sakar a shirya a bata. Ko a cikin wannan shekararda muke ciki anyita damun irin wannan rashin jituwa harta kai ga mahukuntan fina finai sun shiga lamarin domin dawo da zaman lafiya tsakaninsu saidai hakan bai wani tasiri ba.
A kwanannan ne sai dayan jarumin wato Adam A Zango ya fara janyewa daga rikicin musamman ganin yadda Ali Nuhu baya damuwa da abin sosai ba.
An ga jaruman suna taya junansu murna a kafafen sadarwa wanda hakan yana nuni da cewa sun dauki hanyar sulhu wanda babu wanda yakirasu domin su shirya sune dakansu suka yanke wannan hukunci.
A wani rubuta da Zango ya wallafa ya kira wannan rikicin nasu da jarabtar ubangiji kuma yayi Allah wadai da munufukai masu haddasa husuma a masana'antar.
Rikicin tsakanin Ali Nuhu da Adam A Zangi yana shafar cigaban Kannywood ta kowace fuska saboda yadda daukakarsu da fada aji tafi ta kowa a masana'antar dukda cewa sun samu wasu dayawa daga daraktoci zuwa frodusoshi wadanda suka rikede zuwa yaransu daga baya.
Ma'abota kallon fina finan Hausa na cigaba da jindadin da kuma fatan alkhairi ga wannan hadakar dukda cewa ba yanzu suka fara batawa su shirya daga baya ba.


