Wata tattaunawa ta wakana tsakanin malaman addini a nigeria.
Malaman sun hada da Shugaban kungiyar IZALA ta kasa Sheikh Abdullahi Balalau tareda Sakataren kungiyar Sheikh Muhammad Kabir Gombe da kuma Sheikh Yakubu Musa Katsina.
A bangaren malaman Dariqa kuma akwai Sheikh Tijjani Bala Kalarawy da kuma babban d'an Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya wakilceshi.
Sau dayawa ana samun banbance banbancen raayi tsakanin mabiya Dariqa da Izala musamman a shafin sada zumunta wanda hakan ke jawo karuwar rabuwar kai tsakanin mabiya addnin musulunci.
A wuraren taruka dayawa malamai suna haduwa su zauna suci abinci suyi raha sannan su tashi su watse ba tareda tsegumu ko batanci ga junansu ba.
Shin meyasa sai a wurararen wa'azi kadai malamai suke iya batanci ga junansu maimakon lokacin ganawar sirri da suke?
Dayawan mabiya akidu sun dauka yadda ake rura wutar gaba haka take azuciyar malamai wanda koda akwai hakan dayawansu hassadace ke janyo fada tsakaninsu.
Zai wahala ace Dariqa da Izala su hadu wuri guda amma idan ansa tsoron Allah a lamarin to zasu iya zama a kasa 1 su rayu cikin zaman lafiya da bautar Allah.
Babu abinda yadace ga mabiya addini sai su koma ga Allah kuma suyi watsi ga duk wasu munanan akidu da zaa dorasu akan tsanar 'yan uwansu.
Yanada kyau kowa ya nemi ilimi da zai banbance tsakanin gaskia da karya ta yadda wasu bazasu tasirantu da duk wata mara gurbin akida ba.
Hadin kai shine komai a zaman wannan duniya babu abinda yakai ace alumma sun hada kai waje guda don cigaban duniyarsu da kuma lahirarsu. Dukda cewa abu ne mai wahala amma da ace alumma zasu hada kai koda don gyara dubuyarsu ne to da duniyar tayi kyau bare ace sunyi ne don gyaran lahira.
Rashin hadin kai yana cutarda alumma kuma yana rufe duk wata kofa ta samuwar zaman lafiya a doron kasa.
Muna rokon Allah ya karawa alummar musulmu hadin kai da kuma zaman lafiya tsakaninsu.

