Sau dayawa cunkoso yakan haifarda hatsaniya da salwantar rayuka a wurin gudanarda aikin hajji. Saidai a bana an samu sauye sauye a tsarin wanda yasa aka gudanarda aikin batareda samun matsaloli kamar shekarun baya ba.
Jami'an tsaro sun taimaka sosai wajen kula da mahajjata da kuma basu agajin gaggawa aduk inda suka samu matsala.










