UNICEF ta karrama jarumi Ali Nuhu

Kungiyar masu bada agajin gaggawa ga lafiyar yara kanana ta tarayyar turai wato (Unicef) ta karrama jarumi Ali Nuhu bisa namijin kokarinsa wajen shiga harkokin kare hakkin bil adama. 

Taron karramawar ya gudana ne yau alhamis a birnin Kano wanda yahada manyan manyan mutane ciki harda Kwamishinan lafiya na jihar Kano. 

Ministry lafiya ta jihar kano itama ta nuna jindadinta ga jarumin Ali Nuhu inda ya sake samun wata karramawar ga hukumomin lafiya na jihar Kano.

Ali Nuhu shine jarumi mafi shahara a Kannywood wanda ya jima ana damawa dashi ba tareda tauraruwarsa ta dusashe ko sau 1 ba a tarihin masana'antar.