A mako 2 daya suka gabata ne aka fara rikici tsakanin mawakiyya Hauwa 'Yar Fulani Gombe da kuma jaruma Teema Makamashi dalilin wata waka ta Shugaba Buhari wacce Hauwa rera a watannin baya.
Teema Makamashi tayi video wakar ne da shigar fulani tareda masu taka rawa a bayanta dukkansu cikin suturar fulani kamar yadda wakar ma a harshen fulatanci aka rerata.
Hajiya Hauwa tayi karar Teema Makamashi ne saboda kotu ta bi mata hakkinta na daukar wakarta ayi video ba izininta abinda ta kira da an rainata ne shiyasa ba'a nemi izininta ba.
Hauwa ta bayyana cewa kwananan zatai video wakar har ta gama shiri kwatsam sai taga an videon wakar batareda saninta ba.
Teema Makamashi kuma ta bayyana cewa ba don komai tayi videon ba sai don kaunar shugaba Buhari bata tunanin abin zai zama haka ba da batayi ba.
Kungiyar masu ruwa da tsaki Kannywood sun kira dukkan matan biyu sun sasantasu. Sannan kungiyar Kannywood ta kira Teema Makamashi tayi mata nasiha da gargadi an kuma bukaci Teema ta fito ta bayyanawa duniya ba ita tayi wakar ba kuma teema ta fito tayi hakan a shafinta na Instagram.
Saidai kuma bayan sasanta rikicin kuma matan biyu sun sake samun sabani inda Hauwa tace ta fasa hakura sannan kuma ta mayarda karar Teema kotu don neman a hukunta Teema Makamashi.

Masu kallo da bibiyar shafukan sada zumunta suna cigaba da sharhi da kira ga sauran alumma su guji satar fasahar wani yin hakan babban laifi ne a hukunce.


