Saraki ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Nigeria a 2019

Shugaban majalisar dattawan Nigeria Senata Bakola Saraki ya bayyana aniyar neman shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a shakarar 2019.

Saraki ya bayyana aniyarsa ne a yau alhamis lokacin gudanarda wani taro da akayi a otel din Sheraton dake Abuja.

Taron ya gudana ne karkashin inuwar nan da taba matasa damar shiga harkokin siyasar nigeria wato #NotTooYoungToRunBill.

Jam'iyyar PDP na cigaba da shiga sarkakiya yayinda zaben fidda gwani ke karatowa domin tsayarda dan takara da zai kara da shugaba Buhari a zaben 2019.