Tsohon shugaban Nigeria Chief Olusegun Obasanjo ya bayyana komawarsa jam'iyyar PDP wacce ya fice daga cikinta a shekarun baya.
Obasanjo ya bayyanawa manema labarai cewa ya fita daga jam'iyyar ne a abaya saboda rigingimu da suka addabi jam'iyyar wanda yake ganin 'ya'yan jam'iyyar sunyi masa laifi saidai ayanzu kuma an daidaita ya yafe duk abinda akai masa a baya.
Obasanjo ya dawo jam'iyyar ne tareda dayawan membobinsu na jamiyyar ADC wacce ya kafa a kwanakin baya.
A baya bayannan kuma ne suka samu sabani da Shugaba Buhari abinda ya ingiza Obasanjo komawa cikin harkokin siyasar kasar.

