Nigeria tafi kowacce kasa yawan talakawa a duniya -UK Prime Minister

Prime Minister kasar Burtaniya Therasa May ta ayyana Nigeria matsayin kasar data fi kowacce kasa yawan talakawa a dunjya.

Theresa May kusan 'yan Nigeria milyan 87 ke rayuwa da abinda baiwuce dala 1 ba wacce take daidai Naira 350 a kudin Nigeria. 

Theresa tace wannan abin takaici ne ace kasa mai arziki kamar Nigeria amma ta kasa bada mafitar rayuwa ga 'yan kasa hakan bai faye faruwa a sauran kasashe masu arzikin man fetur.

"Africa ya kasance yanki da yakeda arziki saidai rikice rikice kamarsu BOKO HARAM da ISIS da sauran kungiyoyin ayyukan ta'addanci sun addabi nahiyar shiyasa kullum maimakon jindadi sai wahaka ke karuwa acikinta dukda yadda tattalin arzikin wasu kasashen ke karuwa cikin sauri.

Abin farinciki daya ne daga 2015 zuwa 2030 Africa zata doke jerin kasashe dake samun cigaban tattalin arziki cikin gaggauwa a duniya kuma shine abinda zaisa adadin arzkinta ya karu  cikin sauri fiyeda kowacce nahiya a duniya.

A ranar laraba ne dai Therasa ta kawo wata ziyarar cinikayya tsakanin Burtaniya da Nigeria inda ta gana da Shugaba Buhari a birnin tarayya Abuja.

Therasa May ta karkare da cewa kasashen turai zasuyi iya kokarinsu a bana don ganin Africa ta samu cigaba da kuma tallafi don magance matsalar talauci a kasa