Kungiyar masu Luwadi da Madigo ta kasar Ghana zatayi babban taro wanda bata bayyana inda za'a gudanarda taron ba.
Rahotanni sun bayyana cewa za'ayi taron ne don karawa juna sani da kuma wayarda kai ga maza da mata wadanda keda dabiar Luwadi ko Madigo.
Shugaban kungiyar Moses Foh-Amoanin yace "taron zai taimakawa masu dabiar don sanin 'yancinsu da kuma yadda zasu kaucewa hatsarin rashin fahimta dake tsakaninsu da sauran alumma.
"A kalla mutane 400 sunyi regista daga fara sayarda form din wannan kungiyar kuma sunyi ne saboda shirin koya musu yadda zasuyi rayuwa da kowa ba tare da hantara ba.
Wata majiya mai karfi a jihar ta bayyana cewa majalisar kasar bata amince da Luwadi da Madigo ba kuma tana iya kokarinta don ganin ta dakile shirin auren jinsi a kasar.

