Mataimakin gwamnan ya sanar da murabus din nasa ne a wata wasika da ya mika ma gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.
A cikin wasikar, ya ce ya so ya cigaba da rike mukamin mataimakin gwamna har zuwa karshen wa'adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar:
"Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.
A cikin wasikar, ya kara da cewa, "Idan baka manta ba mai girma gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba."
A baya bayan nan ne mataimakin gwamnan ya rubuta wata wasika ga hukumomin tsaron Najeriya, inda yake neman da su dauki mataki akan abin da ya kira wata barazana da jami'an gwamnatin jihar Kano ke yi ga lafiyarsa.
SOURCE: BBC HAUSA

