Martanin Shehu Sani akan kalaman Donal Trump ga Buhari

Senatan mai wakiltar kaduna ta kudu SHEHU SANI ya mayarda martani kan batun nan dake yawo a kafafen sadarwa wanda wasu jaridu suka wallafa cewa Shugaban kasar Amurka Donal Trump yaci mutuncin takwatlransa Shugaba Muhammadu Buhari.

Shehu Sani yace zai wahla wannan batu ya zama gaskia saboda yadda bayanin yazo ta baibai.

Shehu Sani yace" Batun da ke yawo na ganawar Shugaba Trump da yace Buhari kamar gawa yake batu ne kawai na 'Yan jaridu masu yanken magana. Inba haka ba meyasa ba'a dauko batun tun lokacin ganawarsu ba sai bayan watanni hudu.

Haryanzu dai batun nan ne ke yawo kuma alummar nigeria suna cigaba da tofa albarkacin bakinsu akan lamarin.