Makafi masu digiri suna zanga zanga a kofar gidan gomnatin jihar IMO

Zugar matasa makafi wadanda suka kammala karatun jami'a sun kewaye kofar gidan gomnatin jihar IMO suna kiran Gomnan jihar Rochas Okrocha akan rashin kulawa dasu da kuma samar musu aikin yi. 

Makafin sun kewaye gidan gomnatin ne suna korafin cewa gomnati bata lura dasu kuma ana musu wariya wajen daukar aiki a jihar. 

Shugaban kungiyar makafin ya bayyana cewa akwai makafi dayawa a jihar wadanda sun kammala karatun digiri amma basuda aikinyi saboda gomnatin tana nuna halin ko in kula akan su. 

Yace "Gomnatin jihar nan bata gina makaranta ko 1 ba don karatun makafi dukda alkawarinda tayi mana shekara 7 da duka wuce. 

" A watan January muka aika sakon bukatunmu ko kuma muyi zanga zanga amma gomnati bata ce mana uffan ba. Don haka yanzu gamu munzo kuma bazamu je koina ba har sai an biya mana bukatarmu. 

"Muna bukatar adadin kudade milyan 4 kuma muna bukatar a samawa matasa makafi ayyuka. 

"Dukda nakasarmu muka daure mukayi karatu kamar yadda masu ido sukayi to mezaisa bazaa samar mana aiki ba? Shin 
anason muje muyi bara ne? 

An ruwaito wasu mukarrabai a gomnatin jihar IMO sun fito suna baiwa makafin hakuri amma sunki amincewa suna ihun yau kam sai an biya musu bukatarsu. 

Haryanzu dai gomnatin jihar bata maida martani ba kan bukatarda matasan suke nema da kuma abinda suka kira rashin adalci tsakaninsu da masu ido.