Jarumai 2 da baza'a manta dasu ba a masana'antar Kannywood


1. Aminu Sharriff Momo haifafen jihar Kano ne yanada shekara 41, tauraruwarsa ta fara haskawa ne acikin fim din "Ukuba" da aka bashi lambar yabo a shekarar 2001.
 Momo shahararen dan wasan fina finai kuma kuma dan jarida mai gabatarda shiri a gidajen telebijin. Momo jarumi ne da zai iya baka mamaki cikin kankanin lokacin idan yana actin acikin fim musamman fim irin da mugunta ko munafurci momo yakan iya taka rawa da zaj iya sa ka shantake ka manta kallon fim kake ba zahiri ba. 

2. Ibrahim Maishinku haifafen jihar kano ne yanada shekara 42, ya fara fitowa ne a fim din "Saki Reshe" kuma ya samu lambar yabo ta farko a shekarar 2003.
Maishinku dan wasan fina finai ne kuma dan kasuwa, Yanada kwarewa sosai a fina finai irin na zamantakewar aure da kuma rayuwa. Ya kasance jarumi mai nutsuwa da sanin yakamata wanda ake ganin yana daga cikin masu mutunci a idon duniya a jerin wadanda suke a masana'antar Kannywood. Haryau ba'a taba haska wani fim na Maishinku yana rawa ba hakan yasa dayawan masu kallo ke ganin kamar kamun kai ne yasa baya shiga rawa acikin fina finansa. 

Wadannan jarumai 2 baza'a taba mantawa dasu ba a masana'antar fina finan Hausa dama nigeria baki daya saboda irin gudunmawa da suka bayar ga cigaba wajen yada al'adu da harshen HAUSA.