Hukumar zaben Nigeria INEC ta sanarda cigaba da yin rijistar katin zabe har zuwa ranar 17 watan August da zata ruder rijistar a duk fadin nigeria.
Solomon Soyebi Kwomishinan zabe kuma shugaban kwamiti dake wayarda kan mutane a fannin zabe yace sun yanke hukuncin ne bayan wata tattaunawa da suka gudanar a abuja.
Soyebi yace za'a rufe rijistar amma wadanda sukayi zasu cigaba da karbar katin zabensu har zuwa sati 1 kafin gudanarda zaben a Nigeria.
Ya kuma yi kira ga 'yan Nigeria da basuda katin su daure suje suyi rijiata kafin a rufe wadanda sukayi kuma suje su karba da zarar katin ya fito.
Hukumar INEC itace hukumar dakeda alhakin duk wani abu daya shafi zabe a Nigeria.

