Tsohon gomnan jihar kano kuma dan takarar shugabancin kasa a Jam'iyyar PDP Senata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jin dadinsa gameda abinda gomnati tayi na hanashi gudanarda taron tsayawarsa takara a filin Eagle Square Abuja.
Kwankwaso yayi Allah wadai da hanashi filin taron abinda ya kira da rashin adalci da kuma nunawa duniya wannan gomnati bataso wani mahaluki yayi takara da ita.
Wata majiya daga manyan magoya bayan kwankwaso ta ce da gangan aka hanasu filin saboda a muzguna musu dukda cewa sunbi duk wani tsari da akebi don karbar filin kuma da farko mahukuntan filin sun basu receipt wanda suka biya kudi naira milyan 2 da dubu dari 7.
Majiyar ta kara da cewa yanzu haka sunada wani fili da zasuyi taron dama sun tanadeshi don irin wannan matsala idan ta faru.
Magoya bayan Kwankwasiyya sunce dama sun san za'a rina hakan ya nuna karara cewa akwai hannun shugaba Buhari a rashin adalci da ake yiwa Kwankwaso tun lokacinda ganduje ya hanashi shiga Kano a bara shekarar 2017.
Dubban magoya bayan Kwankwaso daga dukkan sassan kasarnan ne suke cincirindo zuwa a abuja tun farkon satinnan domin halartar taron wanda za'a gabatar a yau laraba 29/8/2018.

