Shugaban majalisar dattawan Nigeria Bokala Saraki yace maganar tsigeshi da ake bata taba hanashi bacci ba.
Saraki yace" Abinda yasa bandamu ba shine wadanda sukeson a tsigeni sun nuna hassadarsu karara maimakon subi hanya mai kyau da kundin tsarin mulkin kasa "Constitution" ya tanadar domin tsige shugaba ko nada shi.
Senata saraki yafadi hakan ne yayin zantawa damanema labarai birnin asaba dake jihar Delta yayin wata zantawar sirri da gwamnan jihar Ifeanyi Okowa a gidan gomnati.
Ganawar tasu ta kwashe tsawon mintuna 40 sirrance.
Saraki ya samu rakiyar wasu senatoci kamar Dino Melaye, Peter Nwoaboshi da sauransu. Wannan shine karo na farko da shugaban majalisar ya kai ziyara jihar bayan ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar PDP.
Saraki ya kara da cewa" Bazamu zauna a majalisa ba har sai mun tabbatarda mun duba kasafin kudi da aka warewa zaben 2019 saboda koda mun zauna rikicin tsigewa da fita daga jam'iyoyi shi dabaibaye majalisar.
"Bana tsoron a tsigeni kwata kwata saboda muna rayuwa ne a kasa wacce duk 'yan kasar sun san akwai doka wacce sukayi imani ita zata zartarda komai tun daga shugabanni zuwa talakawan kasa.
A karshe dai saraki ya shawarci gomnan jihar daya maida hankali kan abubuwa da zasu kawo cigaba da kuma zaman lafiya a jaharsa.

