Rundunar 'Yan sandan jigar Edo sun kama wata yarinya mai shekara 23 da laifin sayarda jaririnta saboda ta sayi babbar wayar Android.
Kwamishinan 'yan sanda Mr. Jonson Kokumo ya tabbatarda aukuwar lamarin kuna yace hakan babban laifi ne ga kundin tsarin kasa da kuma hakkin 'yan adam.
Yarinyar mai suna Miracle Johnson tana zaune ne a Agenebode dake karamar hukumar Etsako East local government a jihar Edo. Ta sayarda jaririn nata ne bisa sharadi za'a bata kudi hannu kuma an biyata kudin.
Miracle tace amsa laifinta saidai tace lamarin ya faru ne sakamakon halin kunci da Kuma rashin kulawa da mijinta yake nunawa gareta.
Miracle tace" Na sayarsa jinjirina ne saboda samarwa kaina abin dogaro dakai kasancewar mijina bai damu da halinda nake ciki ba.
"An haifi jaririn ne a ranar 4 watan july kuma na sayarda jaririn ne saboda shawara da wata makwabciyarmu ta bani cewa in sayarda jaririn in nemi Sana'a da kudin.
"Na sayarda jaririn a gidan marayu a matsayin kudi N200,000 kuma ban sayi komai da kudin ba sai waya wacce makwabciyar tamu ta tilasta saina daya.
"Naso in baiwa mijina kudin ya sayi babur ko yayi Sana'a ko zamu sauki akan talauci da muke ciki amma ina tsoron ya gane.
A bangaren mijin nata yace ta taba fada masa zata sayarda jaririn amma bai amince ba yace tayi hakuri karta aikata.
"Bayan ta sayo wayar ta kirani ta fadamin nayi tir da wannan aiki nata kuma na katse wayar saboda yadda cikina ya kadu sakamakon wannan aika aika.
Yanzu haka dai Miracle tana hannun jami'an hukumar 'Yan sanda don karasa gudanarda bincike kafin kotu ta yanke hukuncin abinda ya dace akanta.
PUNCH NEWSPAPER

