Uwargidan shugaban kasan Nigeria Aisha Buhari ta samu karramawa daga jami'ar Sun Moon University dake Asan, South Korea.
Aisha ta karbi karramawar ne daga shugaban jami'ar Dr. Sun-jo Hwang wanda ya mika mata karramawar.
An baiwa Aisha digirin digir-gir ne a fannin nazarin Falsafa (Philosophy).
Aisha Buhari ta mika sakon godiya a shafinta na Facebook inda ta bayyana jindadinta kuma ta godewa mahukuntan jami'ar bisa wannan karramawa.




