Fitacciyar jaruma Zainab Indomie da aka jima ba'aji duriyarta ba.
zata dawo cikin masanaantar fina finai don sake damawa a karo na biyu.
Zainab wacce tayi tashe sosai a shekarun baya tayi batar laya baa sake jin labarinta ba sai kwanannan da jarumi ADAM A ZANGO yaketa dora hotunanta a kafafen sadarwa da nufin cewa zai dawo da ita don tallafa mata da nuna halaccinsa gareta.
Abaya dai A Zango shine babban abokin taka rawarta har ana tunanin soyayya tsakaninsu amma a kwanannan ya sake jaddada cewa babu soyayya tsakaninsa daita saidai yanason taimaka mata musamman ganin yadda wadanda suka moreta suka gujeta.
Adam A Zango ya bayyana yadda yake tausayin Zainab da son cigabanta ya kuma kuduri aniyar dawo da martabarta cikin masanaantar fina finan Hausa inshaAllah kamar yadda ya ambata a shafinsa na #instagram
Zainab Indomie tayi fice sosai a fagen fina finan soyayya da zaman aure ta taka rawa mai yawa wasu manyan fina finai musamman na darakta Aminu Saira.
Kamarsu: Walijam, Ga duhu ga haske, Garinmu da zafi da s
Masu kallo dai sun sanya ido suka alwashin Zangon ko zai tabbata tunda dai dama irin wannan ikirarin ansha yiwa wasu jaruman amma basa dawowa matsayinsu saboda ba kowa ke rasa daukaka ya dawo daita ba.

