'Yan sanda sun kewaye gidan Saraki da mataimakinsa Ekwremodu

'Yan sanda dauke da manyan makamai sun kewaye gidan shugaban majalisar dattawa Bakola Saraki dana mataimakinsa Ekweremodu.

Wannan ya biyo bayan wata wasika da jamian yan sanda suka aikawa Bakola Saraki wasika dake dauke da tambayoyinda sukeso ya amsa kan batun wasu yan fashi da kwanakin baya suka fasa wani banki sannan suka kashe wasu mutane a Offa dake jihar Kwara. 

Masu sharhi suna ganin yakamata Saraki ya fito ya bayyana gaskiya kan abinda ake zarginsa.

Ku biyomu domin sauraron yadda lamarin ke wakana.