An cafke matumin ne mai ikirarin malumtar addinin musulunci a jihar lagos bisa zargin fyade.
Matumin mai suna MUSTAPHA MUHAMMAD mai shekara 25 wanda yake ikirarin malumtar addini an kamashi ne da laifin fyade ga wata daliba a makarantar FEDERAL COLLEGE OF EDUCATION dake Okaka, Lagos.
Kwamishinan 'yan sandan jihar lagos EDGA IMOHIMI, ya bayyana cewa matashin wanda aka fi sani da suna ALFA ya yaudari yarinyar ne ya dauketa zuwa Ikorodu inda yayi mata lalata da ita karfi da yaji.
ALFA ya yaudareta ne da ilimin cewa ya duba yaga zuwa awanni 24 zata mutu. Daga nan yanemi ta bishi domin ya tseratar daita daga mutuwarda yace zatayi bayan zuwansu ikorodu ne ya tilasta mata tarayya dashi.
An ruwaito mahaifan yarinyar ne suka lura da yadda diyar tasu take tafiya da kuma muamala sannan suka tilasta mata sanar dasu abinda ya faru daita.
Kwamishinan ya kara da cewa bayan ALFA akwai wasu mutane 2 dake hannunau wadanda suka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi kuma tare da ALFA din zaai mikasu zuwa kwato don yanke musu hukunci.
Via #NAN

